Gidauniyar ASR Ta Tallafawa Mata 500 Da Abinci A jihar Kaduna

...Tallafawa Marasa Galihu Shine Burina – Inji Hajiya Ummulkhair

Daga Shehu Yahaya 

Gidauniyar Abdul Samad  Rabi’u  ( ASR) ta rabawa mata 500 tallafin abinci domin rage radadin kuncin rayuwa. 

Gidauniyar ta ASR wanda Gidauniyar tallafawa marayu da marasa galihu ta Ummuameena Global Foundation ta jagoranta ta bayyana cewa sun yanke shawarar tallafawa matan ne domin rage musu radadin kuncin rayuwa da shine irinsa na farko a jihar Kaduna. 

Shugaban  Gidauniyar ta Ummuameena wacce ta jagorancin rabon kayan abincin Hajiya Ummulkhair Bukar Kashim, tace tsarin rabon kayan tallafinsu ya sha bambam Dana gwamnati bisa irin kyakkyawar tsari da suka samar na tabbata da cewa sun raba abinci da wadanda suka samu zasu dan Dade suna amfani da shi ba Wai cin rana daya.

Ta ce ” Mun raba musu shinkafa mai nauyin Kg25 da wake mai nauyin kg 20 da taliya guda goma da makaroni guda goma da kuma Jakar ledar ruwa da kayan dandanon girki da girki da kuma Man girki duk mun saka musu a ciki. Babu abinda mace zata nema na girka da babu a ciki illa kawai ta nemi itacen girki kawai”

” Ba jihar Kaduna bane kadai muka raba irin wannan, munyi a jihar Zamafara da Sakkwato da Katsina suma duk mutane dari  biyar- biyar suka amfana da tallafin. Yanzu kuma muna shirin zuwa jihohin Arewa Mason gabas da kuma Arewa ta tsakiya insha Allah “

“Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad Rabi’u dama ya saba tallafawa marasa galihu Amma wannan lokaci Sai ya bamu alhakin jagorantar rabon kayan tallafin wanda kuma munyi iya bakin kokarinmu wajen tabbatar da cewa al’umma sun amfana kuma suna San barka” inji ta.

Hajiya Ummulkhair Bukar Kashim,  ta bayyana  gamsuwarta dangane da kokarin Gidauniyar ASR bisa Bawa Gidauniyar ta alhakin rabon kayan tallafin tana mai bada tabbacin cewa zasu ci gaba da bada tasu gudunmawar wajen taimakon alumma baki dada.

Hajiya Ummulkhair,  taci gaba da cewa ” Dama ni nasa tallafawa marayu da marasa galihu a fadin kasar nan wanda yanzu Ina tunani fadada shirin zuwa kasashen ketare wadanda suke fama da matsalolin ‘Yan gudun hijara da dai sauransu”

Hakazalika,  tace burin Gidauniyar ta shine tallafawa rayuwar al’umma musamma marasa galihu wadanda suke neman tallafi, a cewarta, a haka ta taso tana anyi a gidansu kuma haka zata ci gaba har tsawon rayuwarta.

Akan Hakan ta bukaci gwamnatocin kasar nan da suyi koyi da irin matakan da ASR suke bi wajen bayar da tallafi ga alumma, a cewarta, idan aka bi irin matakinsu da yawan al’umma zasu amfana da tallafin gwamnati. 

Leave a comment