Majalisar Dokokin jihar Kaduna Ta Fara  Bincike Na Musamman Akan Gwamnatin Tsohon Gwamna Jihar  El-rufai

Daga Shehu Yahaya



Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta fara gabatar da bincike na musamman game da yadda Tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i ya gudanar da harkar mulkin sa, musamma a fannin sha’anin kuɗi.

A wata takarda da ta fito daga Akawun Majalisar, Sakinatu Hasan ta bayyana cewa binciken da za a fara yi wa Tsohon Gwamnan sun shafi basussuka, mu’amular kuɗi da harkar kwangilolin da ya bayar a zamanin yana Gwamna.

Kwamitin da Majalisar ta kafa don gudanar da wannan bincike, zai binciki shekaru takwas da El-rufa’i ya yi a kan mulki.

Cikin wannan takarda da Akawun Majalisar ta fitar, wacce kuma ta miƙa wa Kwamishinan kuɗi na jihar, ta jadadda masa cewa binciken zai mayar da hankali ne a basussuka, mu’amalar harkokin kuɗi, kwagilolin da ya bayar, waɗanda aka biya da waɗanda ake bin jihar bashi, a duk faɗin shekaru 8 na mulkin nasa.

Akawun ta bayyana cewa, “Majalisar  Dokokin jihar Kaduna, a zamanta na 150, wanda ya guda ranar Talata 16 ga Afrilu, 2024 ta zartar, tare da kafa Kwamitin da zai binciki basussuka, mu’amular kuɗi, kwagilolin da ake bin jihar bashi, da abubuwan da suka shafi wannan, na gwamnatin jihar Kaduna tun daga 29 ga Mayun 2015 har zuwa 29 ga Mayun 2023.”

Wasu daga cikin bayanan da  Majalisar ke buƙata daga Ma’aikatar kuɗin jihar, sun haɗa da:

(i) Duk basussuka: Cikakkun bayanai daga watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2023, taren da shaidar amincewar Majalisar Dokokin jihar Kaduna, da kuma asusun da aka sanya waɗannan basussuka, da cikakken bayani daga sashen manyan kuɗaɗe da na kula da bashi.

(ii) Rahoton zaman Majaliasar zartarwar da aka amince da ciwo ba shin.

(iii) Biyan kuɗaɗen kwangiloli: cikakken bayani game da kuɗaɗen kwangilolin da aka biya, da waɗanda ‘yan kwangila ke bi bashi a tsakanin Mayun 2015 da Mayun 2023.

(iv) Albashin ma’aikata: rahoton albashin da aka biya ma’aikatan jijar, tun daga shekarar 2016 zuwa 2022,

(v) Rahoton Hukumar tara kuɗaɗen shiga: Rahoton Hukumar tara kuɗaɗen shiga daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Sai kuma ƙa’idoji da wa’adin basussukan da aka karɓo.

Leave a comment