Ganduje  Shi Ke Yada Cewa Na Bar APC .. Inji Kwankwaso 

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta labaran da ke yawo a shafukan yanar gizo cewa ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

Kwankwaso ya bayyana cewa, wannan wata  kutungwila da gwamnatin jihar Kano Abdullahi Umar Handier  ke yi domin bata ma shi suna.

Mai magana da yawun Kwankwaso Aminu Abdussalam, ya ce babu kamshin gaskiya a cikin batutuwan, domin Sanata Kwankwaso bai taba tunanin fita daga jam’iyyar APC ba.

Aminu ya kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ce ta watsa labarin don kawai ta shafa wa Kwankwaso kashin kaji, biyo bayan tabbatar da Umar Doguwa a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar APC.

Ya ce Kwankwaso da tawagar sa ba su taba tunanin barin APC zuwa wata jam’iyya ba, abokan hamayya ne kawai su ka kitsa labarin, sakamakon tsoratar da su ka yi da yawan magoya bayan Sanata Rabi’u Musa Kwanwkaso.

Leave a comment