Masu Tada Zaune Tsaye Zasu Fuskanci Fushin Hukuma…. Inji Samuel Aruwa


Gwamnan jihar kaduna Malam Nasir El-Rufa’i  ya ja kunnen al’umman jihar da su daina yada rade-radi da ka iya tada zaune tsaye a jihar musamman a karamar hukumar Kajuru da sauran sassan jihar.

Sannan kuma ya bukaci mutane da su daina amfani da shafukan zumunta musamman Facebook wajen yada hotunan da ka iya tada rikici a jihar.

Da yake jawabi mai magana yawun gwamnan jihar Samuel Aruwan a wata takarda da sanya ma taken El-Rufai ya ce duk mutumin da aka kama da laifin haka zai fuskanci hukunci.

Akalla mutanen 33 suka rasa rayukansu a rikicin Kajuru wanda mafi yawansu Fulani ne.

Gwamnatin ta ba Jami’an tsaro a jihar damar kamo wadanda ake zargin da rura wutan rikici a jihar.

Gwamnatin ta da tabbacin cewa lallai za ta hukunta duk wanda ta samu yana da hannu a rikicin da ya faru a karamar hukumar Kajuru.

Leave a comment