BIKIN SALLA: Da Alamu Raguna Zasu Yi Kwantai 


A daidai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 4 a gudanar da bukukuwan babbar sallah, raguna na nan jibge a kasuwanni babu masu siya .A wannan shekarar, da dama daga cikin masu sayan raguna da wuri-wuri kamar yadda aka saba a baya, ba su halarci kasuwa ba har zuwa yanzu.

Masu sayar da dabbobi a kasuwanni sun ce, duk da kudaden ragunan sun banbanta da na bara ,ba a zuwa ana saya sosai.

Masu siyan ragunan da yanzu suka siya, sun shaida wa manema labarai cewa, farashin ragunan a bana da sauki idan aka kwatanta da na bara.

A bara dai-dai sai da aka kai raguna sayarwa a kasuwanin Jamhuriyar Nijar daga Najeriya sanadiyar tabarbarewar darajar da Naira ta yi.

Tambayar ita ce, shin ko a bana ma saboda rashin cinkin raguna yayin da Sallah ke karatowa zai sa ‘yan kasuwa fita da ragunan nasu zuwa kasashen waje makwabta?

Leave a comment